28 Agusta 2020 - 13:33
​ Faransa Ta Yaba Wa Yarjejeniyar Da Iran Da IAEA Suka Cimma

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Faransa, ta yaba da yarjejeniyar baya bayan nan da Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta cimma da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya.

ABNA24 : Da yake sanar da hakan ministan harkokin wajen kasar ta Faransam Jean Yves Le Drian, ya ce hakan wata hanya ce mai kyau, kuma yana daga cikin alkawuran dake cikin yarjejeniyar nukiliyar da Iran din ta cimma da manyan kasashen duniya.

Dama kafin hakan kasashen Rasha da China, sun yada da yarjejeniyar da Iran din ta cimma da hukumar ta IAEA.

A ranar Laraba data gabata ne gwamnatin Iran tare da hukumar makamashin nukiliya ta duniya suka sanar da cimma matsaya kan wasu muhimamn batutuwa ciki harda wadanda kasashen yamma suka jima suna ta korafi a kai.

An cimma yarjejeniyar ce yayin ziyarar kwanaki biyu da shugaban hukumar ta IAEA, Rafael Grossi ya kawo a nan Tehran.

Daga cikinsu akwai cewa Iran ta amince da bai wa Hukumar, damar binciken wasu cibiyoyi biyu da ake zargin tana bunkasa makamashin nukiliya cikinsu a asirce.

342/